Abinda yasa Amurka ta rufe ofisoshinta

Ayman Al-zawahiri
Image caption Kasar Yemen ta fitar da sunayen mutane 25 da ta ce suna shirin kai ma ofisoshin kasashen waje hare-hare.

Wata hira da aka ce wasu manyan shugabannin kungiyar Al-qaeda sun yi ta waya wadda aka nada a asirce, ita ce ta sa Amurka rurrufe ofisoshin jakadancinta masu yawa a kasashen musulmi ranar lahadi.

Hirar wadda Shugaban Kungiyar Ayman Al-zawahiri yayi da wani, ta kunshi wani shirin kai hari mafi ban tsoro tun bayan hare-haren sha daya ga Satumba, inji kafafen watsa labaran Amurka. Da farko dai Amurkar ta ce ta rufe ofisoshin dake arewacin Afrika da Gabas ta Tsakiya ne domin karin kandagarki.

A wajen wasu tarukan yiwa 'yan jarida bayani, fadar White House da kuma Ma'aikatar Harkokin wajen Amurkar sun ce barazanar ta fito ne daga kungiyar Al-Qaeda a Tsibirin Larabawa (AQAP). Sai dai sun ki su yi wani karin bayani.

Ofisoshin Jakadancin Amurkar da aka rufe a biranen Abu Dhabi, da Amman, da Alkahira, da Riyadh, da Dhahran, da Jiddah, da Doha, da Dubai, da Kuwait, da Manama, da Muscat, da Sanaa da kuma birnin Tripoli; za su ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa ranar Assabar

Karin bayani