'Yan tawaye sun kwace wani sansani a Aleppo

Image caption 'Yan tawayen Syria

Rahotanni daga Syria sun ce 'yan tawaye sun kama wani sansani na mayakan sama dake arewacin Aleppo bayan an shafe watanni ana gumurzu kansa da sojojin gwamnati.

Wata kungiyar kare hakkin 'yan kasar Syria dake Britaniya ta ce sansanin na mayakan sama dake Mannagh dab da kan iyaka da kasar Turkey ya fada hannun 'yan tawayen ne bayan an shafe sa'o'i 24 ana gwabza kazamin fada.

Bayanai sun nuna cewar an kashe mutane da dama a dukkan bangarorin biyu.

Masu aiko mana labarai sun ce, idan aka tabbatar da kwaatar sansanin, rashinsa zai hana hukumomin Syria samun kafar da za su rinka kai ma mayakan 'yan tawaye hari dake cikin lardin Aleppo.

Karin bayani