Kiran sassantawa tsakanin 'yan Masar

Senatoci McCain da Graham da Chambliss
Image caption Taron sassanta kasa ne kawai zai samar da zaman lafiya a Masar

Sanatocin Amurka biyu John McCain da Lindsay Graham sun yi kiran da a saki fursunonin siyasa a kasar Masar.

Bayan sun zanta da jami'an gwamnati a birnin Alkahira, Sanata McCain ya ce shawarwarin sulhu ba za su yiwu ba yadda ya daace muddin Shugabannin jam'iyyar 'yan uwa Musulmi suna tsare a gidan yaari.

Ya ce kamata ya yi a ce an sanya kowa da kowa a sasantawar ta kasa, yana mai cewa ita ce hanyar kawai da za a samu zaman lafiya a kasar.

Ya nemi a kira taron sasantawa na kasa wanda zai kunshi jam'iyyar ta 'yan uwa musulmi, da kuma gaggauta komawa shirin democradiyya.

Karin bayani