Indiya ta zargi Pakistan da kashe sojanta 5

Sojan indiya a Kashmir
Image caption Indiya da Pakistan sun gwabza yaki sau biyu kan yankin na Kashmir.

An kashe sojojin Indiya biyar a wani hari da aka kai kan iyakar kasar da Pakistan da suke rikici a kai wato yankin Jammu da Kashmir.

Sojojin India sun zargi sojin Pakistan da hannu a harin.

Sojin na Indiya sun ce sojojin Pakistan sun yi wa jami'an nasu kwanton- bauna ne bayan sun tsallaka kan iyaka.Pakistan ta yi watsi da wannan zargin.

Harin ya zo ne kwanaki kalilan bayan kasar Pakistan ta bada shawarar a koma tattaunawar zaman lafiya da Indiya wanda aka dakatar tun watan Janairu.

An dai dakatar da tattaunawar ne bayan an kai hari shigen wannan inda aka sare kan wani sojan Indiya.

Karin bayani