Bakin haure na gararamba a Malta

Wasu daga cikin bakin hauren Malta
Image caption Wasu daga cikin bakin hauren Malta

Gwamnatin Malta ta ki amincewa ta kyale wani jirgin ruwan dakon mai dauke da wasu bakin haure 'yan Afrika su sama da dari ya tsaya a tasharta.

Hakan watsi ne da kiran da Hukumar Tarayyar Turai ta yi ma ta na ta yi hakan, tana mai cewa akwai nauyi a kanta na ta kayle fasinjojin su sauka bisa dalilai na jinkai.

An ceto bakin hauren ne daga tekun Bahar Rum.

Jami'an soja Malta da suka shiga jirgin ruwan sun ce babu wani cikin bakin hauren da ke cikin hadari, ciki har da mata masu ciki.