Musharraf bai halarci zaman kotu ba

Pervez Musharraf
Image caption Musharraf dai shi e yayi wa Firayi minista mai ci yanzu Nawaz Sharif juyin mulki a 1999.

Tsohon shugaban mulkin sojin kasar Pakistan Pervez Musharraf bai halarci zaman kotu ba a birnin Rawalpindi domin fuskantar tuhamar da ake masa ta kisan tsohuwar Firayi Ministar kasar Benazir Bhutto a shekarar 2007.

Lauyan Mr Musharraf, Ilyas Siddiqi, ya shaidawa BBC cewa hukumomin birnin ba su da isassun kayan aikin da za su kare Mr Musharraf don haka babu tabbas wajen kare lafiyarsa.

Duka biranen Rawalpindi da Islamabad dai na cikin shirin ko ta kwana saboda rahotannin da ke cewa akwai yuwuwar kai hare-hare daga 'yan takife.

An dai dage sauraren karar ta Mr Musharraf zuwa ashirin ga wannan watan.

Karin bayani