Yau laraba take Sallah a Nijar

Taron Idi a Kano
Image caption A kusan kowace shekara dai akan samu sabani tsakanin kasashe wajen bukukuwan na Sallah

A yau Laraba ne ake bukukuwan karamar sallah a Jamhuriyar Nijar, bayan da musulmin kasar suka kammala azumin watan Ramadana ranar Talata.

'Yan kasar ta Nijar dai sun dauki azumi ne ranar Talata 9 ga watan Yuli gabanin wasu kasashen musulmi irinsu Najeriya da Saudiyya inda sai ranar 10 ga watan Yulin ne aka soma azumin.

Sai dai yayin da suke shirye-shiyen bukin sallar, iyalai da dama na kokawa kan rashin isassun kudaden yin sayyayar kayan sallah kamar yadda aka saba duk shekara.

Magidanta da dama kuma sun koka kan tashin gwabron zabi da farashin kayyakin masarufi yayi a daidai sa'adda ake fara azumin.

Karin bayani