An kashe jami'an tsaron Pakistan 3

Sojan Pakistan
Image caption Pakistan dai ta jima tana fama da hare-hare daga mayakan Taliban

An kashe akalla jami'an tsaron Pakistan uku a wani hari da aka kai a yankin Gilgit-Baltistan da ke yankin arewa mai nisa na kasar.

Jami'an da suka hada da dansanda daya da sojoji biyu na kan hanyar su na ta zuwa wani taron na tsaro a lokacin da aka yi wa motar su kwanton- bauna.An jiwa wasu da dama rauni a harin.

Da yake hira da BBC, kwamnadan jami'an tsaron yankin Ajmal Bhatti wanda shi ne zai gana da jami'an, ya ce suna kan bincike, kuma ya zuwa yanzu babu wanda ya yi ikirarin kai harin.

An kai harin ne a daidai wurin da aka kashe mutane goma a watan Yunin da ya gabata ciki har da masu yawon bude idanu 'yan kasashen waje tara.

Karin bayani