'Zan warware takaddamar nukiliyar Iran'

Image caption Shugaba Hasan Rouhani na Iran

Sabon Shugaban Iran, Hasan Rouhani ya sha alwashin warware takaddamar dake tattare da shirin nukiliyar kasar Iran.

A jawabinsa ga manema labarai a karon farko tun da aka rantsar dashi a ranar Lahadi, Mista Rouhani ya ce a shirye yake ya shiga tattaunawa mai ma'ana tsakaninsa da kasashen yammacin duniya.

Amma a cewarsa, Iran nada 'yancin habakka ayyukanta na ma'adanin uranium.

Rouhani ya ce za a warware matsalar ta hanyar tattaunawa, bawai ta hanyar barazana ba.

Ya kuma soki Amurka wanda ya ce, maganarta daban, sannan abinda take aikatawa daban.

A cewarsa, har yanzu Amurka ba tada cikkakkun bayanan lamaran dake faruwa a Iran.

Karin bayani