Taarabt zai koma Fulham daga QPR

Image caption Dan Morocco, Adel Taarabt

Kocin Fulham, Martin Jol ya bayyana cewar dan kwallon Queens Park Rangers, Adel Taarabt na gabda zuwa kulob dinsa a matsayin aro.

Dan kwallon Morocco mai shekaru 24, a ranar Talata za a gwada lafiyarsa.

Taarabt zai koma Fulham ne saboda yana bukatar buga wasan Premier League bayanda QPR ta koma gasar Championship.

Jol ne kocin Tottenham lokacin da ya siyo Taarabt daga kungiyar Lens ta Faransa a shekara ta 2007.

Taarabt ya bugawa QPR wasanni 31 a kakar wasan data wuce, inda ya zira kwallaye biyar.

Karin bayani