Zamu kafa gwamnatin hadaka- Mullah Omar

Image caption Mullah Omar

Shugaban kungiyar Taliban a Afghanistan, Mullah Omar ya ce ba za su kankane mulki ba, idan dakarun kasashen waje suka fice daga cikin kasar a badi.

A wata sanarwa daya fitar na bukin karamar Sallah, ya ce kungiyar Taliban za ta zauna da al'ummar Afghanistan don kafa gwamnatin hadaka wacce za ta bi tsarin addinin musulunci.

Mullah Omar wanda yake boye tun shekara ta 2001, ya bayyana cewar bata lokaci ne kawai, zaben da za a gudanar a shekara mai zuwa a kasar.

Amurka ta ce duk wanda ya bata bayanan yadda za ta kamashi, za ta bashi dala miliyon goma.

Kungiyar Taliban ce keda alhakin galibin hare-haren da ake kaddamarwa a Afghanistan.

Karin bayani