An haramta zanga-zanga a Uganda

shugaba Yoweri Museveni
Image caption Gwamnati ta ce dokar za ta taimaka wajen kare kowa da kowa.

Majalisar dokoki a Uganda ta amince da wata sabuwar doka mai cike da rudaani wadda ta haramta zanga-zanga.

An amince da dokar ne duk da kakkausar suukar da ta sha daga kungiyoyin kaare hakkin dan adam da na addini da 'yan majalisa 'yan adawa da kuma jama'ar kasar.

A karkashin sabuwar dokar, 'yan sanda za su iya fasa taron mutum ukku kadai ko fiye da haka wadanda ke tattauna batutuwa na siyasa a cikin gidajensu.

Prime Ministan kasar ta Uganda Amama Mbabazi ya ce an bullo da dokar ne don taimakawa wajen baiwa 'yan sanda ayyukan da suka daace.

Ya kara da cewa a karkashin tsarin mulkin kasar ta Uganda an dora ma 'yan sanda alhaki ne na kaare doka da oda, su kaare kowa da kowa, har da su kansu wadanda ke son sauke 'yancinsu na yin zanga-zangar.

Karin bayani