An bukaci a saki fursunonin siyasar Masar

Mohammed Morsi
Image caption Ana dai ci gaba da tsare Mohammed Morsi tun bayan tumbuke daga kan mulki a farkon watan jiya.

'yan majalisar dattawan Amurka da ke wata ziyara a kasar Masar, wato John McCain da Lindsay Graham sun bukaci a saki fursunonin siyasar da ake tsare da su a kasar.

Bayan tattaunawa da jami'an gwamnati a birnin Alkahira, Sanata McCain ya ce ba za a samu kyakkyawar sasantawa da shugabannin kungiyar 'yan uwa musulmi ba alhali su na gidan kaso.

Ya bukaci tattaunawar sulhu ta kasa baki daya, da za ta hada har da kungiyar ta 'yan uwa musulmi, da kuma komawa kan tsarin Dimokradiya cikin sauri.

Mr Graham ya ce Masar ta zurfafa cikin rikicin da ya kai dan'uwa na kashe dan'uwansa, abinda ya sa kowa ke yi wa kasar kallon wadda ta fada cikin rudani.

'yan majalisar biyu dai na ziyara Masar ne bisa umarnin Shugaba Obama.

Karin bayani