Yemen ta tsaurara matakan tsaro

Image caption 'Yan kasashen waje sun fice daga Yemen

Gwamnatin kasar Yaman ta fito da wasu matakan tsaro da ba a taba ganin irinsu ba kan gine-ginen gwamnati da wasu manyan cibiyoyi domin rigakafin hare-hare daga kungiyar Al-Qaeda.

Rahotanni sun ce an ga tankoki da motocin sulke kusa ga fadar Shugaban kasa, kuma hukumomi sun kafa wuraren bincike a duk sassan babban birnin kasar Sana'a; inda ake bincikar motoci da mutane musamman da dare.

Hakama an bukaci manyan jami'an gwamnati, da kwamandojin soji da na wasu hukumomin tsaro da su sa ido kuma su takaita yawace-yawace.

Sai dai gwamnatin kasar ta Yemen ta soki kasar Amurka da kawayenta kan janye ma'aikatan ofisoshin jekadancinsu daga kasar sakamako samun rahotannin barazanar kai harin.

Wata sanarwa da ofishin Jakadancin Yaman a birnin Washington ya fitar tace wannan matakin na kwashe jami'ai jakadancin, biyan bakatar masu tsattsauran ra'ayi ne kuma zagon kasa ne ga hadin kan da Yemen ke baiwa al'ummar kasa da kasa wajen yaki da ta'addanci.