An umurci Amurkawa su fice daga Yemen

Image caption Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry

Amurka ta umurci wasu daga cikin ma'aikatan ofishin jakadancinta su fice daga Yemen, ba tare da bata lokaci ba.

Sannan kuma ta bukaci Amurkawa suma su bar kasar ta Yemen.

Ofishin Sakataren harkokin wajen Amurka ne ya bada gargadin, saboda barazanar ayyukan ta'adanci da ake fuskanta a Yemen.

Wannan gargadin na zuwa ne 'yan sa'o'i bayan da jiragen Amurka marasa matuka suka kashe wadanda ake zargin mayakan Alka'ida ne a Yemen su hudu.

Gwamnatin Birtaniya ta ce itama za ta janye ma'aikatan ofishin jakadancinta na wucin gadi daga Yemen har sai abubuwa sun kyautatu.

Karin bayani