Soja ya damfari gwamnatin jihar Bayelsa

Image caption Ana zargin aikata cin hanci a rundunar sojin Najeriya

Wata kotun soji ta musamman a Najeriya ta yanke wa wani jami'inta mai mukamin laftanar kanar daurin shekara bakwai a gidan kaso.

Kotun ta sami Laftanar kanar R A Ahangba da laifin damfarar gwamnatin jihar Bayelsa naira miliyon dari da hamsin.

Kotun soji ta musamman din, wadda Janar Edward Nze, tare da taimakon Keptin Chukudi Okonkwo ya jagoranci zamanta, ta bayyana cewa laftanar kanar R A Ahangba ya karbi tsabar kudi naira miliyon dari da hamsin bisa alkawarin taimaka wa tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva wajen ganin ya yi tazarce a zaben gwamna da aka yi a jihar na shekara 2011.

Kotun dai ta ce abin da jami'in ya yi rashin da'a ne kuma ya saba da tarbiyyar aikin soja.

Sai dai lauyan jami'in da aka dauren ya ce za su daukaka kara, saboda a cewarsa akwai wasu batutuwa da shari'ar ba ta tabo ba.

Karin bayani