Fasinjoji sun gamu da cikas a Nairobi

Image caption Gobarar ta yi barna a Nairobi

Gobara ta lashe wani yankin filin tashi da saukar jiragen sama na Kenya, lamarin daya tilasta rufe shi.

Wutar ta janyo tsaiko a zirga-zirgar jiragen sama a yankin gabashin Afrika.

Daruruwan fasinjoji sun yi cirko-cirko a wajen filin saukar jiragen sama na Jomo Kenyatta dake Nairobi wanda shine aka fi hada-hada a cikinsa a fadin yankin gabashin Afrika.

Yanzu haka jirage sun koma sauka a birnin Mombasa.

Kawo yanzu babu rahoton wadanda lamarin ya rutsa dasu, amma hukumomin Kenya sun ce an shawo kan gobarar.

Sai dai kuma wadanda suka shaida lamarin sun ce 'yan kwana-kwana basu tinkari lamarin cikin gaggawa ba.

Karin bayani