An nemi Cameron da ya taimaka

Wadanda suka gabatar da takardun a wajen 10 Downing Street
Image caption Wadanda suka gabatar da takardun a wajen 10 Downing Street

An mika wasu takardu dauke da jerin sa hannun mutane fiye da dubu 25 ga fadar Pira ministan Burtaniya, wadda a ciki suke kira ga David Cameron da ya taimaka wajen ceto wasu kamfanonin aike da kudade zuwa kasashe masu tasowa.

A ranar Litinin mai zuwa ce dai, aka shirya bankin Barclays zai rufe assusun ajiya na wadannan kamfanoni, abun da zai kawo karshen ayyukansu.

Bankin na Barclays dai yana nuna damuwa cewa wasu daga cikin kamfanonin ba su da fasahar gaano miyagun ayyuka, saboda haka za su iya taimakawa ba tare da saninsu ba, wajen ba wasu mutane damar daukan nauyin ayyukan ta'addanci ko kuma halalta kudaden haram.

Daga cikin wadanda suka hannun har da yar majalisar dokokin Burtaniya, karkashin jam'iyyar Labour, Rushanara Ali da kuma fitaccen dan gudun nan na dogon zangon dan asalin Somalia, Mo Farah.