Syria: An kashe 'yan tawaye 62

Image caption Gaburbura a Syria

An kashe akalla mayakan 'yan tawaye sittin da biyu sakamakon kwantan baunar da dakarun gwamnatin Syria suka yi musu.

Kungiyar 'yan adawa ta Syrian Observatory for Human Rights ta ce lamarin ya auku ne a kusada garin Adra dake gabashin Damascus.

Kungiyar ta ce "mutane 62 galibi matasa, sun yi shahada a hannun sojin gwamnati".

Kamfanin dillancin labarai na Syria-Sana bai bada adadin wadanda suka rasu ba, amma yace 'yan tawayen na bangaren al-Nusra Front ne wato kungiyar dake da alaka da Alka'ida.

Majalisar dinkin duniya ta kiyasta cewar mutane fiye da dubu dari daya sun mutu a tashin hankalin da ake yi a Syria cikin watanni 28.

Karin bayani