Amurka da Rasha za su gana a Washington

Barack Obama da Vladimir Putin

Ministocin tsaro da kasashen waje na Amurka da Rasha, za su hadu a birnin Washington a yau Juma'a.

Kwanaki kadan bayan da shugaba Obama ya soke ganawarsa da shugaba Vladimir Puttin na Rashar.

kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ta ce tattaunawar ta su ta yau Juma'a za ta tabo batutuwa da dama.

Ciki kuwa har da batun matakin da Rashar ta dauka, na baiwa mai kwarmata bayanan sirrin Amurka, Edward Snowden mafakar siyasa, lamarin da Amurka tayi Allawadai dashi.

Wakilin BBC a birnin Washington ya ce zai zama abu mai wuya ga kasashen biyu su cimma matsaya, saboda yadda dangantaka tsakaninsu take kara tsami.

Karin bayani