An haifi Jaririya mafi girma a Spain.

jaririya mafi girma da aka haifa a spain
Image caption jaririyar da mahaifiyarta ta haifa ba tare da shan wahala ba.

Wata mata 'yar Burtaniya ta haifi jaririyar da ta fi kowacce girma a Spain da kanta.

Yarinyar da aka haifa wadda baban ta dan asalin Colombia ne, nauyin ta ya kai kilo shida da digo biyu.

Ana haifar jarirai masu girma a kasar Spain ta hanyar tiyata, amma mahaifiyar yarinyar 'yar shekaru Arba'in ta haife ta salin-alin ba tare da ta bukaci ko allurar rage radadin nakuda ba.

An sanyawa jaririyar suna Maria Lorena Marin, kuma likitoci sun ce ita da mahaifiyarta suna cikin koshin lafiya.