An kai hari Quetta a Pakistan.

Mutane a wani masallaci a pakistan
Image caption 'Yan bindiga sun kai hari masallacin quetta a pakistan

An kai wani hari wajen masallaci a birnin Quetta da ke kudu masu yammacin Pakistan, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane takwas.

Kafar yada labaran Pakistan ta rawaito cewa 'yan bindigar da ba a san ko su waye ba, sun so kai harin ne kan wani dan siyasar yankin Ali Madaad Jaatak,.

Amma ya tsira ba tare da ya ji rauni ba.

Harin ya zo ne kwana daya bayan da wani dan kunar bakin wake ya kai wani hari da ya hallaka kimanin mutane tara a birnin.

Karin bayani