'An karyata kai hari a kan motocin Assad'

Image caption Shugaba Assad a masallacin Idi

Ministan yada labaran Syria ya karyata zargin 'yan tawaye cewar an kai hari a kan ayarin motocin Shugaba Bashar al-Assad.

Omran Zoabi ya ce rahotannin da suka ce an harba makamin roka a kan ayarin motocin "mafarki ne kawai".

'Yan tawaye sun ce sun harba roka a kan ayarin motocin a lokacin da shugaban kasar ke kan hanyarsa ta zuwa masallacin Anas bin Malik a yankin Malki, kusada inda gidan Shugaban kasar yake.

Hotuna sun nuna Mista Assad babu abinda ya same shi bayan kamalla Sallar Idi a wani masallaci a Damascus bayan kamalla azumin watan Ramadan.

Tunda farko, Islam Alloush na bangaren mayakan Liwa al-Islam, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewar an kaiwa ayarin motocin shugaban kasar hari a lokacin da yake tafiya masallaci a babban birnin kasar.

Karin bayani