Spain na bincikar hadarin jirgin kasa

Tutar kasar spain
Image caption kimanin mutane saba'in da tara ne suka rasa rayukansu a hadarin jirgin kasa a spain a watan da ya gabata

Mutane biyu da suke kula da tashar jiragen kasa za su bayyana a gaban majalisar dokokin Spania a yau alhamis, domin amsa tambayoyi game da hadarin jirgin kasar da ya faru a kasar a watan da ya gabata, da ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane saba'in da tara.

Za a tambayi shugabannin kan matakanda suka dauka dan kare lafiyar matafiya a jiragen kasa.

Ana sa ran za a kuma tambaye su matakin da za su dauka na sadarwa tsakanin ma'aikatan jirgin da kuma kamfanoni.

A yanzu dai an maida hankali ne akan bincikar direban jirgin, wanda ya ke magana da abokin aikinsa ta wayar tarho jim kadan kafin jirgin ya kauce hanya.

Karin bayani