Masar: Ana bikin Idi cikin zaman dar-dar

Image caption Amurka da tarayyar turai sun yi kira ga dukkan bangarorin biyu da su sasanta kansu.

Ana cikin halin zaman tankiya a kasar Masar a daidai lokacin a ke soma bukukuwan karamar sallah bayan kokarin da wasu kasashe suka yi na warware rikicin ya wargaje.

Gwamnatin da rudunar sojin kasar ta daure wa gindi na barazanar daukar mataki kan wasu sansanonin zanga-zanga biyu dake makare da magoya bayan hambararren shugaban kasar Mohammed Morsi.

A cikin sakonsa na sallah, shugaban rikon kwarya na kasar Mansour Adliy, ya bayyana Masar a zaman kasar da ke cikin wani mawuyacin yanayi.

Kafin wannan jawabin ya dora alhaki rugujewar kokarin shiga tsakani na kasa da kasa domin warware kiki-kakar siyasar kasar kan kungiyar 'yan Uwa Musulmi.

Farayin minista Hazem Beblawi yayi gargadin cewar babu ja-da-baya ga shawarar da gwamnatinsa ta yanke ta rufe sansanonin.

Wani shugaban kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ya ce barazanar za ta iya kai ga kisan-kiyashi; amma zanga-zangar da suke zata ci gaba.

Karin bayani