Neman ganin karshen takunkumin kan Iran

Fursunonin siyasar Iran
Image caption Daga cikin fursunonin har da Faeza Hashemi, mai fafutukar kare 'yancin mata kuma 'yar tsohon shugaban kasar Rafsanjani.

Fursunonin siyasar Iran fiye da Hamsin sun yi kira ga Shugaba Barack Obama da ya kawo karshen takunkuman da aka saka wa kasar kuma yayi anfani da abin da suka kira dama ta karshe ta kawo karshen takaddama tsakanin Amurka da Iran.

A cikin wata wasika da aka wallafa cikin jardar Guardian ta Burtaniya ranar jumu'a, jagororin 'yan adawar sun nemi Obama da yayi anfani da damar da zaben Hassan Rouhani a zaman shugaban kasar Iran mai sassaucin ra'ayi domin sasanta kasashen biyu.

Wadanda suka sa hannu kan wasikar dai sun soki takunkuman da Amurka ta kakabawa Iran din wadanda suka ce sun jefa rayuwar talakawa kasar cikin mawuyacin hali.

'' Mun yi imani cewar lokaci yayi da kasashen mu biyu za su bude wani sabon babi domin soma sabuwar tafiya ta fahimtar juna.'' Inji wasikar wadda fursunoni 55 da suka hada da tsofin jami'ai, da masu fafutuka, da 'yan jarida, da kuma 'yan tawaye suka rattaba wa hannu.

Karin bayani