Ganawa tsakanin Palasdinawa da Isra'ila

Image caption Obama na shiga tsakanin Netanyahu da Abbas

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanarda cewar za a soma tattauna gaba da gaba tsakanin Isra'ila da Palasdinawa a birnin Kudus a ranar Laraba.

Sannan kuma su kara wata tattaunawar a garin Jericho dake gabar yamma da kogin Jordan.

Wannan shine zai kasance sasantawa ta farko tsakanin bangarorin biyu cikin shekaru uku.

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya ce bangarorin biyu sun amince su cimma yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya cikin watanni tara masu zuwa.

A cewar Mista Kerry duka bangarorin za su tabbatar da bukatunsu a lokacin zaman.

Karin bayani