An maido da zirga-zirzar jirage a Nairobi

Image caption An dai juya akalar jiragen da ke fitowa daga wasu kasashe ne zuwa filayen jiragen da ke biranen Eldoret da Mombasa.

Hukumomin kula da filaye jiragen sama a Kenya sun tabbatar da cewar an maido da tashi da saukar jiragen kasa da kasa a filin jirgin saman Jomo Kenyatta inda wata gagarumar gobara ta tashi ranar laraba da safe wadda ta kone wasu sassansa.

Wani jirgin da ya taso daga birnin London shi ne ya fara sauka a filin jirgin da misalin karfe shida da rabi na safe agogo kasar inji wani wakilin BBC.

''Hakama wasu jirage daga biranen Bankok da Kilmanjaro su ma sun sauka a filin jirgin da safenan.'' inji shi

Tun a ranar larabar ne dai Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta bayar da sanarwa maido da zirga-zirgar jirage ta cikin gida da kuma ta jiragen dakon kaya a filin jirgin, wanda ke da matukar muhimmanci ga yankin inda fasinjoji sama ga 16.000 ke sauka ko tashi a kowace rana.

''Bincike na gudana''

Har yanzu dai ba a tabbatar da sanadin gabarar ta sanyin safiya ba. Sai dai gwamnatin Kenyar ta bukaci matafiya da yan kasuwa da su ba ta lokaci su kuma yi hakuri domin jami'an tsaro na ci gaba da bincike domin gano musabbabbin wannan gagarumar gobara wadda ta haddasa hasarar dimbin dukiya.Kafafen watsa labaran Kenya na sa ka alamar tambaya, akan me yasa aka dauki tsawon lokaci ba a kashe gobarar ba, saboda rahotannin da ke cewa masu aikin kashe gobarar sun fuskanci karancin ruwa da kayan aiki.