Al'ummar Musulmi na bukukuwan Sallah

Image caption Eid-el-fitr dai shi ne biki na biyu mafi girma ga musulmi.

Miliyoyin musulmi a duk fadin duniya sun soma shagugulan biki mai tsarki na Eid-el-fitr wanda ke nuna kawo karshen azumu watan Ramadana.

Wannan dai ya biyo ne bayan sanarwar ganin watan Shawwal da hukumomin addinin Musulunci na kasashen daban-daban suka bayar ranar Laraba da dare.

A Najeriya, kasa mafi yawan al'ummar musulmi a Afirika ta Yamma, shugaban majalisar koli ta addinin musuluncin kasar ne ya bayar da sanar wa ganin watan a fadar dake birnin Sokoto da daren Larabar.

Bukukuwan sun kunshi ibada, da saka sabbin tufafi da kuma ziyarce-ziyarce 'yan uwa da abokai.

Sai dai tuni wasu musulmin suka soma bukukuwan tun ranar laraba saboda labarin ganin watan da suka samu tun daren ranar Talata, yayinda wasu kasashen za su fara a ranar jumu'a saboda rashin ganin watan.

Karin bayani