An kashe mutane 29 a Pakistan

Image caption Bam ta yi kaca-kaca da wata mota

Wani dan kunar bakin wake ya kashe mutane kusan ashirin da tara sakamakon bam din daya tada lokacin jana'izar wani dan sanda a birnin Quetta dake yankin kudu maso yammacin Pakistan.

Lamarin kuma ya janyo jikkatar mutane fiye da hamsin.

Jami'an 'yan sanda sun ce galibin wadanda suka rasu, da kuma wadanda suka samu raunuka 'yan sanda ne wadanda suka halarci jana'izar.

Kakakin 'yan sanda, Mir Zubair Mehmood ya ce dan kunar bakin waken ya tada bam din gabda a soma Sallar gawan.

Jami'an 'yan sanda sun ce daga cikin wadanda suka mutu hadda shugaban bangaren gudaarwa na 'yan sanda a Baluchistan, yankin da ake dade ana fama da matsalar tsaro.

Karin bayani