Amurka ta umurci ma'aikatanta su bar Lahore

Image caption Tambarin ma'aikatar harkokin wajen Amurka

Amurka ta umurci galibin ma'aikantan ofishin diplomasiyyarta su fice daga birnin Lahore na Pakistan.

Wani jami'in Amurka ya ce umurnin ya biyo bayan barazanar da karamin ofishin jakadancin Amurka ke fuskanta a cikin birnin.

Haka nan ya umarci 'yan Amurka da su dakatar da duk wata tafiya da ba ta zama dole ba zuwa Pakistan.

Jami'ai a Amurkar sun ce wannan matakin baida alaka da dalilan da suka tilastawa Amurka ta rufe ofisoshin diplomasiyyar ta dake gabas ta tsakiya da arewacin Afrika.

Wakilin BBC a Islamabad ya ce hukumomi a Pakistan sun saka babban birnin a cikin shirin kota kwana, saboda fargabar tsaro musamman a gine-ginen gwamnati.

Karin bayani