'An tafka kura-kurai a zaben Zimbabwe'

Image caption Shugaba Robert Mugabe

A karon farko hukumar zaben kasar Zimbabwe ta amince an samu kura-kurai a zaben da aka gudanar a makon daya wuce.

A cewar hukumar zaben, kusan masu zabe dubu dari uku ne aka hana kada kuri'a a ranar zaben.

Hukumar zaben ta kara da cewar mutane kusan dubu dari biyu an canza musu ra'ayi wajen kada kuri'a.

Amma a cewarta, kura-kuran basu kai a soke nasarar zaben da Shugaba Robert Mugabe ya yi ba.

Shugaban 'yan adawa, Morgan Tsvangirai ya yi zargin an tafka magudi inda yace zai kalubalanci sakamakon zaben a kotu.

Karin bayani