Kotu ta yankewa dan Bangladesh hukunci

Image caption Quazi Nafis

Kotu ta yankewa wani dan kasar Bangladesh hukuncin daurin shekaru talatin a gidan yari saboda yinkurin dasa bam a ofishin babban bankin Amurka a New York.

Quazi Mohammad Rezwanul Ahsan Nafis, wanda ya amsa laifinsa, kuma ya nemi afuwa ga al'ummar New York.

Kuma a cewarsa yanzu ya fita daga cikin masu tsatsaurar ra'ayin Musulunci.

An tsare Mista Nafis a watan Oktoban shekara ta 2012 ne, bayan da yayi kokarin tada bam a cikin wata mota da aka ajiye ta a harabar babban bankin Amurka.

Sai dai kuma ashe hukumar tsaro ta FBI ce ta saka abubuwan fashewa na boge a cikin motar.

Lauyoyin Nafis sun ce an cusa masa tsatsaurar ra'ayin Musulunci ne a jami'ar Bangladesh lokacin da yake fuskantar matsalolin rayuwa.

Karin bayani