An sace matuka jirgin saman Turkiya

Image caption Jirgin saman Turkiya

'Yan bindiga sun sace wasu matuka jirgin sama su biyu na kamfanin jiragen saman Turkiya a kusa da filin jirgin sama na Beirut dake Lebanon.

An dauke mutanen da karfi suna cikin mota tare da wasu sauran ma'aikatan jirgin saman Turkish Airline lokacin da suke hanya zuwa masaukinsu daga cikin filin jirgin saman.

Masu aiko da rahotanni sun ce bisa dukkan alamu, lamarin tamkar ramuwar gayya ce sakamakon garkuwa da aka yi da wasu 'yan Shi'a na Lebanon a cikin Syria a shekarar data gabata.

Iyalan 'yan shi'an sun yi murna bayan da suka samu labarin sace mutanen.

Suna zargin cewar gwamnatin Turkiya bata matsawa 'yan tawayen Syria lamba ba don a saki 'yan Shi'an.

Karin bayani