Mutum 6 sun mutu a Saliyo bayan ruftawar gada

Tutar Saliyo
Image caption Gadar na daya daga cikin gadojin da suka zagaye garin

A kalla mutane shida da suka rasa matsugunan su, sun rasa rayukan su a Freetown babban birnin kasar Saliyo bayan da gada ta rufta da su a lokacin da suke bacci.

Wannan lamari dai ya faru ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin da kwarya da akayi.

Wani babban jami'in dan sanda a garin, ya ce ya yi amannar cewa, akwai mutane da dama da yake tunanin ruftawar gadar ya rutsa da su inda jami'an ceto ke kokarin ceto su.

Wakilin BBC a Freetown ya ce, gadar babba ce kuma tana daga cikin gadojin da suka zagaye garin, kuma yawancin wadanda ba su da gidaje kan fake a karkashin ta.

Karin bayani