Jirgin soji ya kama da wuta a Mogadishu

Image caption Jirgin saman na dauke da makamai

Wani jirgin saman soji ya kama da wuta yana kokarin sauka a filin jiragen sama na Mogadishu babban birnin Somaliya.

Dakarun kungiyar tarayyar Afrika- AU wadanda keda sansani a filin jirgin saman, sun ce matuka jirgin su hudu sun mutu sannan wasu mutane biyu sun samu raunuka.

Jirgin saman dai mallakar rundunar sojin saman kasar Habasha ne.

Rahotanni sun nuna cewar jirgin ya dakko makamai ne masu fashewa.

Lamarin ya tilasta rufe filin jirgin saman Aden Adde dake Mogadishu, kuma sai da aka shafe sa'o'i biyu kafin a shawokan wutar.

Karin bayani