An watsama 'yan mata ruwan batur

Image caption Kirstie Trup da Katie Gee

'Yan sanda a Zanzibar sun ce za su bada tukwicin kusan pan dubu hudu ga duk wanda ya bada bayyanan yadda za a kama wasu mahara biyu da suka watsama 'yan mata na Birtaniya ruwan batur.

'Yan matan wadanda 'yan asalin London ne, Kirstie Trup da Katie Gee, an watsa musu ruwan batur a fuska da kirji da hannu a lokacin da suke tafiya da yamma a birnin Zanzibar.

Gwamnatin tsibirin ce ta sanarda tukwicin kudin.

A daren ranar Alhamis ne aka dakko 'yan mata a cikin jirgi daga Tanzania zuwa London don neman magani.

'Yan matan sun je aikin sakai ne a Zanzibar, inda suke kayarwa a wata makaranta.