MDC ta shigar da kara a Zimbabwe

Image caption Mugabe da Tsvangirai

Jam'iyyar adawa a kasar Zimbabwe, Movement for Democratic Change-MDC ta shigar da kara don kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar da aka gunadar a karshen watan daya wuce.

Hukumar zaben kasar dai ta sanarda Shugaba Robert Mugabe na jam'iyyar ZANU-PF a matsayin wanda ya lashe zaben da gagarumin rinjaye.

Ita dai jam'iyyar MDC ta bukaci kotu ta soke zaben saboda abinda ta kira manyan matsaloli da aka fuskanta.

A cewar MDC, nan gaba za ta shigar da kara gaban kuliya don ta kalubalanci sakamakon zaben majalisar dokoki inda jam'iyyar Mugabe ta samu nasara.

A ranar Alhamis, hukumar zaben kasar Zimbabwe ta ce akalla masu zabe fiye da dubu dari uku ne aka hana zabe a rumfunan zabe.

Karin bayani