Wasu 'yan ci-rani sun mutu a tekun Italiya

Jirgin ruwan bakin haure a Italiya
Image caption Jirgin ruwan bakin haure a Italiya

Hukumomin Italiya sun tsamo gawawwaki shidda na 'yan ci-rani da ruwa ya ci.

Karamin jirgin da suke ciki ne ya ci karo da kasa, 'yan mitoci daga bakin teku da ke da 'yan yawon shakatawa, a garin Catania da ke yankin Sicily.

Ma'aikacin bakin teku ya ce akwai yiwuwar mamatan 'yan kasar Syria ne.

Ya kuma ce, kamar karfe biyar da rabi na asuba ne wani mutum ya ba da rahoton cewa wani jirgin ruwan kamun kifi, dauke 'yan ci-rani dari da bakwai ya tunkuyi kasa a bakin teku.

Lamarin ya auku ne a daidai lokacin da wasu jiragen ruwan yawon shakatawa guda uku suka isa Cataniyar, inda safa-safa na masu shakatawar suka cakudu da motocin marasa lafiya da ma'aikatan ceto.

Karin bayani