Jami'an tsaro sun shiga hannu kan kwasar ganima a Kenya

Zauren saukar bakin da ya kone a Kenya
Image caption Zauren saukar bakin da ya kone a Kenya

A Kenya, ana can ana yin tambayoyi ga 'yan sanda bakwai da masu bincike ke zargi da hannu wajen kwasar ganima, a lokacin da wuta ta lalata zauran saukar baki na Babban Filin Jirin Saman birnin Nairobi a wannan makon.

'Yan sandan, wadanda suka hada da mai mukamin sufeto, ana zargin su ne da satar kudi da giya.

Ma'aikatan shige da fice, da ma'aikatan filin jirgin, da direbobin tasi, su suna cikin wadanda kyamarorin tsaro suka dauke suna sata a kantuna.

Hukumomin suna kuma neman wasu mutane hudu da ke jiran tasa keya zuwa kasashen da suka fito, wadanda suka arce a lokacin da wutar ta barke.