Al-Azhar zata tattauna da 'yan siyasar Masar

Masar
Image caption Al- Azhar na yunkurin sasanta 'yan siyasar Masar

Shugaban kungiyar cibiyar mafi girma a Masar wato Al Azhar, ya soma tuntubar al'umma da kuma fitattun 'yan siyasa da ke wakiltar bangarori da dama a cikin kasar da nufin gudanar da wani taro akan sasantawa a kasar.

Akwai fargabar da ake yi game da cewa, za a sami karin zubar da jini, yayin da gwamnatin kasar me samun goyon bayan sojoji ta lashi takobin tarwatsa wasu sansanoni biyu a birnin Alkhahira wanda masu zanga-zanga suka mamaye, inda suke bukatar a dawo da hambararren shugaban kasar Mohammed Morsi kan kujerarsa.

Sakataren majalisar dinkin duniya da Amurka da kuma kungiyar Tarayyar Turai, dukkaninsu sun bukaci Misirawa da su nemo hanyar warware rikicin da ake ciki.

Karin bayani