Al-Shabab ta kwashe kayayyakin gwamnati

Kungiyar mayakan Al -Shabab
Image caption Al-shabab ta fara kai farmaki ne tun shekarar 2011

Ta bayyana cewa, kungiyar masu kaifin kishin Islama ta Al Shabab dake Somalia ta sace wadansu kayayyakin aiki da gwamnatin Burtaniya ta kawo tare da biyan kudin su wadanda suka zarta fiye da dala dubu dari bakwai.

An dai kwashe kayan ne daga dakin ajiyar kayayyaki inda Kungiyoyin agaji dake aiki tare da gwamnatin Burtaniya suke ajjiye kayayakin aikin ofis da kuma kayayyakin agaji

Kungiyar Al-shabab dai ta fara kai farmaki ne tun a watan Nuwambar shekarar 2011, ta kuma shafe watanni ta na haka.

Gwamnatin Burtaniya ta shaidawa BBC cewa, an lalata kusan dukkan kayayyakin agajin a lokacin farmakin.

Karin bayani