'Yan Uwa Musulmi a Masar sun soki Limamin Azhar

Masu zanga zanga a Masar
Image caption Masu zanga zanga a Masar

Jam'iyyar Shugaban Masar, Mursi, da aka hambare, ta yi kakkausar suka ga yunkurin shiga-tsakani da daya daga cikin malaman kasar mafi girma ke yi.

Kakakin harkokin waje na jam'iyyar Mursi ta 'Yanci da Adalci, yana kokwanton samun adalci daga Babban Limanin na Al-Azahar saboda goyon bayan juyin mulkin da ya yi tun farko.

Ya ce , da shi da Paparoma Tawadros duka suna wurin da aka bayyana yin juyin mulkin, lokacin da Marshall Sisi ya yi jawabi ga jama'ar Masar. Kakakin ya kara da cewa magoya bayan Shugaba Mursin za su ci gaba da zanga-zangar ganin an mayar da shi a kan, kuma a shirye jama'a suke su mutu.