An rufe rumfunan zabe a Mali

Wata mata tana kada kuri'a a Mali
Image caption Bayan rufe rumfunan zabe, 'yan Mali suna jiran su ji wanda ya yi nasara

A Mali, an rufe rumfunan zabe a zaben shugaban kasa zagaye na biyu da aka yi ranar Lahadi.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya kawo cikas ga zaben, abin da ya sanya masu sa ido suka yi hasashen fitowar jama'a ba za ta kai ta zagayen farko ba.

Wani mai nazarin siyasa a kasar ta Mali, Demba Boundy, ya yaba da tarin mutanen da suka fito kada kuri'unsu a karon na farko.

"Yanzu karin Maliyawa sun amince ko sun fahimci cewa kuri'arsu tana yin tasiri ko za ta iya yin tasiri.

"Kuma wannan muhimmin gaci ne aka kai, wannan muhimmin lokaci ne ga Mali".

Ana fafatawa ne tsakanin ’yan takara biyu da suka fi samun kuri'u a zagayen farko: tsohon Firayim Minista Ibrahim Boubakar Keita da Soumaila Cisse, tsohon ministansa na kudi.

Karin bayani