Magoya bayan Morsi na ci gaba da zaman dirshan

Tsaro a Masar
Image caption 'Yan uwa musulmi a Masar sun ki barin dandalin da suke

Magoya bayan hanbararren Shugaban Kasar Masar Mohammed Morsi na ci gaba da yin zaman dirshan a dandalin nan guda biyu dake birnin AlQahira duk kuwa da alamun da hukumomi suka nuna na soma fatattakar su.

A daukacin daren jiya, dubun dubutar magoya bayan Morsi sun yi ta rera wakoki suna daga tutar Kasar da kuma hoton hanbararren Shugaban.

Wata majiya a ma'iakatar cikin gida ta Masar ta fadawa BBC cewa dakarun tsaron Kasar sun yi shirin korar masu zanga zangar jim kadan kafin asuba.

Kungiyar 'yan uwa musulmi ta fitar da wata sanarwa a ranar Lahadi wacce ta nuna alamun wani kira ga magoya bayanta da su kakkafa sabbin sansanonin zanga zanga, a yayinda suke kiran da a maida Morsi kan kujerar sa.

Karin bayani