Masar: An ja kunnen magoya bayan Morsi

Ministan harkokin wajen Masar, Nabil Fahmy, ya ce dole magoya bayan shugaban kasar da aka hamɓarar, Mohammed Morsi, su kawo ƙarshen zanga zangar da suke ba tare da ɓata lokaci ba.

Hukumomin Masar sun ce, zaman dirshan din da magoya bayan Morsi suke ci gaba da yi yana kawo cikas.

Ministan ya ce, har yanzu gwamnati na fatan warware lamarin ta hanyar sasantawa, kuma duk wani matakin da za a ɗauka, na tarwatsa masu zaman dirshan ba zai saɓa doka ba.

An yi ta jita-jitar cewa, a yau jami'an tsaro za su kai farmaki akan magoya bayan Morsi, amma har yanzu shiru kake ji.