Indiya ta kera jirgi mai daukar jiragen sama

Jirgin ruwa mai daukar jiragen sama na Indiya
Image caption Za a cigaba da kera jirgin tare da sanya masa abubuwan da yake bukata

A karon farko Indiya ta kaddamar da jirgin ruwa mai daukar jiragen sama a jihar Kerala dake kudancin kasar.

Rahotanni sun ce za a yi ta yin gwajin jirgin da aka sanya wa suna INS Vikrant a shekarar 2016, kafin sojin ruwan kasar su fara amfani da shi a shekarar 2018.

An kaddamar da jirgin mai nauyin tan dubu 37 da 500, a ranar Litinin.

Jirgin mai tsawon kafa 850 da fadin mita 60, an kera shi ne a cikin kasar ta hanyar amfani da karafa masu inganci, wanda masana'antar karafa ta kasar ta sarrafa.

Hakan ya sanya kasar cikin sahun kasashen dake da karfin kera irin wannan jirgin, wato Amurka da Birtaniya da Rasha da kuma Faransa.