Boubacar Keita ya lashe zaben Mali

Ibrahim Boubacar Keita
Image caption Mr. Cisse ya ce ya taya Mr. Keita murna

Tsohon Fira Ministan Kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya lashe zagaye na biyu na zaben Shugaban Kasar bayan da abokin hamayyarsa Soumaila Cisse ya amince da nasarar sa.

Mr. Cisse wanda tsohon ministan kudi ne ya ce ya taya Mr. Keita murna, ya kuma yi masa fatan alheri.

Zaben ya biyo bayan shekaru hudun da aka shafe ana rikici a kasar, wanda ya hada da wani juyin mulki.

Haka kuma sojoji karkashin jagorancin sojojin Faransa sun shiga kasar, domin yakar masu fafutukar Islama da kuma 'yan tawayen Azbinawa wadanda suka kwace iko da arewacin Kasar.

Karin bayani