Shugaban Mexico na neman masu saka jari

Shugaban Mexico
Image caption Mexico na bukatar ta inganta bangaren makamashin ta.

Shugaban Kasar Mexico Enrique Pena Nieto ya nemi a canza tsarin mulkin Kasar domin baiwa kamfanonin mai dana iskar gas masu zaman kansu na Kasashen waje damar kulla kawancen kasuwanci tare da kasar a bangaren makamashi a karo na farko cikin shekaru.

Canje canjen wani bangare ne na wani shiri dake da niyyar jan hankalin kamfanoni masu zaman kansu cikin bangaren makamashin.

Mr. Pena yana kuma so a budewa kamfanoni masu zaman kansu harkokin da suka shafi tace danyen mai da harkar sufuri dama wasu ayyuka da suka danganci wadannan.

An dai maida Kamfanin man kasar Mexico mallakar gwamnati a shekarar 1938 kuma kuri'ar jin ra'ayoyin jama'a na nuna cewa akasarin jama'ar kasar sun gwammace kamfanin ya balle daga gwamnati.

Shawarar da shugaban Kasar ya gabatar ya saba da abinda ake gani a wasu kasashen na Latin Amurka irinsu Argentina da Bolivia wadanda a kwanannan suka mayarda wsau kamfanoni masu zaman kansu mallakar gwamnati.

Dole ne dai sai kudurin dokar ya samu tsallakewa a majalisun dokoki.

Karin bayani