Mugabe ya caccaki 'yan adawa

Image caption Shugaba Mugabe da Matarsa

Shugaban Zimbabwe da aka sake zaba, Robert Mugabe, ya ce 'yan kasar sun zabi demokradiyya, kuma jam'iyyarsa ta ZANU-PF, ba za ta taba yarda nasarar da ta samu ba.

A jawabinsa na farko tun bayan zaben, Mista Mugabe, ya yi watsi da ikirarin 'yan adawa da ke cewa ya saci kuri'ar ne.

Ya ce, idan ba su ji dadi ba, to su 'rataye kansu'.

Jagoran 'yan adawa na jam'iyyar MDC, Morgan Tsvangirai, bai halarci bikin tunawa da 'yan mazan jiyan ba, inda Shugaba Mugabe ya yi jawabin nasa.

Mista Tsvangirai ya shigar da kara kotu, yana kalubalantar sakamakon zaben da mista Mugabe ya lashe da fiye da kashi sittin cikin dari.

Karin bayani